17 Sunansa ya ƙare a gida da a jeji,Ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18 Za a kore shi daga ƙasar masu rai,Za a kore shi daga haske zuwa duhu.
19 Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.
20 Daga gabas zuwa yamma, duk wanda ya ji labarin ƙaddarar da ta same shi,Zai yi makyarkyata, ya yi rawar jiki don tsoro.
21 Wannan ita ce ƙaddarar mugaye,Wannan ita ce ƙaddarar mutane waɗanda ba su damu da kome na Allah ba.”