2 “Ayuba, mutane kamarka sun taɓa yin shiru?Da ka yi ƙoƙari ka kasa kunne da mun yi magana da kai.
3 Me ya sa kake tsammani mu dakikai ne kamar shanu?
4 Cutar kanka kake yi saboda fushin da kake ji.Duniya za ta ƙare ne sabili da kai?Za a kawar da duwatsu sabili da kai?
5 “Za a kashe hasken mugun mutum,Harshen wutarsa ba zai ƙara ci ba.
6 Fitilar da take cikin alfarwarsa ba za ta ba da haske ba.
7 A dā gagau yake tafiya, amma yanzu ɗingishi yake yi,Shawararsa ta kāshe shi.
8 Yana tafiya, sai ya fāɗa cikin tarko.Tarkon ya kama ƙafafunsa.