2 “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu?
3 A kowane lokaci kuna wulakanta ni,Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina.
4 Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne,Da me ya cuce ku?
5 Tsammani kuke kun fi ni ne,Kuna ɗauka cewa wahalar da nake shaTa tabbatar ni mai laifi ne.
6 Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini,Ya kafa tarko don ya kama ni.
7 Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba,Amma ba wanda ya kasa kunne.Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.
8 Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa,Ya rufe hanyata da duhu,