12-13 Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.
14 Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.
15 Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.
16 Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.
17 Zai mutu bai ga kogunan man zaitun ba,Ba kuwa zai ga rafuffukan da suke da yalwar albarka ba.
18 Tilas ya rabu da dukan abin da ya yi wahalarsa.Ba dama ya mori dukiyarsa,
19 Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.