19 Saboda zalunci da rashin kula da matalauta,Da ƙwace gidajen da waɗansu suka gina.
20 “Har abada ba zai kai ga samun abin da yake wahala ba.
21 Sa'ad da ya ci ba zai yi saura ba,Gama yanzu dukiyarsa ta ƙare.
22 A lokacin da yake gaɓar samunsa,Baƙin ciki mai nauyin gaske zai ragargaza shi.
23 Bari ya ci duk irin abin da yake so!Allah zai hukunta shi da hasala da fushi.
24 Lokacin da yake ƙoƙari ya kuɓuta daga takobin baƙin ƙarfe,Za a harbe shi da bakan tagulla ya fāɗi warwar.
25 Kibiya za ta kafe a jikinsaTsininta zai yi ta ɗiɗɗiga da jini,Razana ta kama zuciyarsa.