3 Abin da ka faɗa raini ne,Amma na san yadda zan ba ka amsa.
4 “Hakika ka sani tun daga zamanin dā,Sa'ad da aka fara sa mutum a duniya,
5 Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.
6 Mai yiwuwa ne ya ƙasaita, ya zama kamar hasumiya a sararin sama.Ya ƙasaita har kansa ya taɓa gizagizai.
7 Amma zai shuɗe kamar ƙura.Waɗanda dā suka san shi,Za su yi mamaki saboda rashin sanin inda ya tafi.
8 Zai ɓace kamar mafarki, kamar wahayi da dad dare,Ba kuwa za a ƙara ganinsa ba.
9 Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.