9 Ba za a ƙara ganinsa a wurin zamansa ba.
10 Tilas 'ya'yansa maza su biya zambar da ya yi wa matalauta,Tilas hannuwansa su biya dukiyar da ya ƙwace.
11 Ko da yake gagau yake, ma'aikaci ne kuma sa'ad da yake yaro,Duk da haka ba da jimawa ba, zai zama ƙura.
12-13 Ɗanɗana mugunta yana da daɗi a gare shi ƙwarai,Yakan sa wata a bakinsa don ya riƙa jin daɗin tsotsanta.
14 Amma a cikinsa wannan abinci yakan zama da ɗaci,Ɗacinsa kamar na kowane irin dafi mai ɗaci ne.
15 Mugun mutum yakan harar da dukiyar da ya samu ta hanyar zamba,Allah zai karɓe ta har da wadda ya ci a cikin cikinsa.
16 Abin da mugu ya haɗiye kamar dafi yake,Yakan kashe shi kamar saran maciji mai mugu dafi.