1 Ayuba ya amsa.
2 “Ku kasa kunne ga abin da nake faɗa,Wannan ita ce ta'aziyyar da nake nema a gare ku.
3 Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
4 “Ba da 'yan adam nake faɗa ba,Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.