17 “An taɓa kashe hasken mugun mutum?Ko masifa ta taɓa fāɗa wa wani daga cikinsu?Allah ya taɓa hukunta wa mugu da fushi,
18 Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa?Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?
19 “Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa.A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi.Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
20 Bari dai a hukunta masu zunubiSu kuma ga hasalar Allah.
21 Bayan rasuwar mutum,Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?
22 Mutum zai iya koya wa Allah?Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?
23 “Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,Suna cikin farin ciki da jin daɗi,