19 “Kukan ce Allah yakan hukunta yaro saboda zunuban mahaifinsa.A'a! Allah dai yakan hukunta wa masu zunubi.Ya kuma nuna ya yi haka saboda zunubansu ne.
20 Bari dai a hukunta masu zunubiSu kuma ga hasalar Allah.
21 Bayan rasuwar mutum,Ruwansa ne ya sani ko 'ya'yansa suna jin daɗi?
22 Mutum zai iya koya wa Allah?Mutum zai iya shara'anta wa Allah Mai Iko Dukka?
23 “Waɗansu mutane sukan yi zamansu ba ciwon kome har ranar mutuwarsu,Suna cikin farin ciki da jin daɗi,
24 Jikunansu kuwa sun yi ɓulɓul.
25 Waɗansu kuwa ba su taɓa sanin farin ciki ba.Sukan yi dukan kwanakinsu su mutu da baƙin ciki.