4 “Ba da 'yan adam nake faɗa ba,Ina da isasshen hanzarin da zai sa in yi fushi.
5 Ku dube ni, ashe, wannan bai isa ya sa ku yi zuru,Ku firgita, ku yi shiru ba?
6 Sa'ad da na tuna da abin da ya same ni,Sai jikina ya yi suwu, in yi ta makyarkyata ina rawar jiki.
7 Me ya sa Allah yake barin mugayeHar su tsufa su kuma yi arziki?
8 'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.
9 Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba,Ba su taɓa zama a razane ba.
10 Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,Suna haihuwa ba wahala.