7 Me ya sa Allah yake barin mugayeHar su tsufa su kuma yi arziki?
8 'Ya'yansu da jikokinsu sukan girma a idonsu.
9 Allah bai taɓa aukar wa gidajensu da bala'i ba,Ba su taɓa zama a razane ba.
10 Hakika shanunsu suna ta hayayyafa,Suna haihuwa ba wahala.
11 'Ya'yansu suna guje-guje,Suna tsalle kamar 'yan raguna,
12 Suna rawa ana kaɗa garaya,Ana busa sarewa.
13 Suka yi zamansu da salama,Su mutu shiru ba tare da shan wahala ba.