1 Elifaz ya yi magana.
2 “Akwai wani mutum, ko mafi hikima,Wanda zai amfani Allah?
3 Gaskiyar da kake yi za ta amfani Allah?Ko kuwa abin kirki da kake yi zai taimake shi?
4 Ai, ba don tsoron Allah da kake yi ba ne,Ya sa wannan tsautawa da jarrabawa suka same ka.
5 Ko kusa ba haka ba ne,Amma saboda zunubi mai yawa da ka yi ne.Saboda kuma dukan muguntar da ka aikata.