13 Duk da haka ka ce, ‘Allah bai san kome ba.Gizagizai sun lulluɓe shi, ƙaƙa zai iya yi mana shari'a?’
14 Kana tsammani gizagizai masu duhu sun hana shi gani,A lokacin da yake tafiya a kan iyakar da take tsakanin duniya da sararin sama.
15 “Ka ɗauka a ranka ka bi gurbin da mugaye suke bi kullum?
16 Kafin ma su kai ga kwanakinsu,Sai rigyawa ta shafe su.
17 Su ne mutanen da suka ƙi Allah,Suka kuwa gaskata ba shi da ikon yi musu kome,
18 Ko da yake Allah ne ya arzuta su.Ba na iya gane tunanin mugaye.
19 Mutanen kirki suna murna,Marasa laifi kuma suna dariyaSa'ad da suka ga ana hukunta mugaye.