6 Don ka sa ɗan'uwanka ya biya ka bashin da kake binsa,Ka ƙwace tufafinsa, ka bar shi huntu.
7 Ka hana wa waɗanda suke ji ƙishi ruwan sha,Ka hana waɗanda suke jin yunwa abinci.
8 Ka mori ikonka da matsayinka,Don ka mallaki dukan ƙasar.
9 Ba ƙin taimako kaɗai ka yi ba,Amma har marayu ma ka yi musu ƙwace, ka wulakanta su.
10 Don haka ne yanzu akwai ramummuka ko'ina kewaye da kai,Tsoro ya kama ka nan da nan.
11 An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,Rigyawa ta sha kanka.
12 “Ashe, ba a can saman sammai Allah yake zaune ba?Sai ya sunkuya ya dubi taurari, ko da yake suna can sama ne.