1 “Me ya sa Allah bai tsai da ranar da zai yi shari'a ba?Me ya sa ba ya tsai da ranar adalci gaWaɗanda suka bauta masa?
2 Mugaye sukan ci iyaka,Don su ƙara yawan gonarsu.Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.
3 Sukan saci jakunan marayu,Su kama san gwauruwa,Su ce sai ta biya basusuwanta.
4 Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.
5 Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,Haka matalauta suke,Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.