10 Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.
11 Suna matse mai daga 'ya'yan zaitun.Suna kuma matse ruwan inabi daga 'ya'yan inabi,Amma su kansu suna fama da ƙishi.
12 Kana jin kukan waɗanda suka yi rauni daWaɗanda suke baƙin mutuwa a birni,Amma Allah bai kula da addu'o'insu ba.
13 “Akwai mugaye waɗanda suke ƙin haske,Ba su fahimce shi ba, suka ƙi bin hanyarsa.
14 Da asuba mai kisankai yakan fita ya kashe matalauci,Da dare kuma ya yi fashi.
15 Mazinaci yakan jira sai da magariba,Sa'an nan ya ɓoye fuskarsa don kada a gane shi.
16 Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje,Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.