2 Mugaye sukan ci iyaka,Don su ƙara yawan gonarsu.Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.
3 Sukan saci jakunan marayu,Su kama san gwauruwa,Su ce sai ta biya basusuwanta.
4 Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.
5 Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,Haka matalauta suke,Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.
6 Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.
7 Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.
8 Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.