4 Sukan hana matalauta samun halaliyarsu,Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.
5 Kamar jakunan jeji waɗanda sukan nemi abinci a busasshen jeji,Haka matalauta suke,Ba inda za su iya samo wa 'ya'yansu abinci.
6 Ya zama tilas a gare su su girbe gonakin da ba nasu ba,Su tattara 'ya'yan inabi daga gonakin mugaye.
7 Da dare sukan kwanta, ba su da abin rufa,Ba su da abin da zai hana su jin sanyi.
8 Sukan jiƙe sharkaf da ruwan sama wanda yake kwararowa daga kan duwatsu.Sun takure a gefen duwatsu neman mafaka.
9 “Mugaye sukan bautar da yara marayu,Sukan kama 'ya'ya matalauta a bakin bashin da suke bi.
10 Amma tilas matalauta su fita huntaye, ba sa da abin sutura.Tilas su girbi alkama suna kuwa jin yunwa.