1 Ayuba ya amsa.
2 “Kai ne mai taimakon marar ƙarfi,Kai ne mai ceton rarrauna!
3 Kai ne kake ba marar hikima shawara,Kai kake sanar da ilimi mai ma'ana a wadace!
4 Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka?Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana?