5 “Lahira tana rawa,Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro.
6 Lahira tsirara take a gaban Allah,Haka kuma Halaka take a gaban Allah.
7 Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum,Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba.
8 Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa,Girgijen kuwa bai kece ba.
9 Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa.
10 Ya shata da'ira a kan fuskar teku,A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu.
11 Ginshiƙan samaniya sun girgiza,Sun firgita saboda tsautawarsa.