2 “Na rantse da Allah Mai Iko Dukka,Wanda ya ƙwace mini halaliyata,Wanda ya ɓata mini rai.
3 Muddin ina numfashi,Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
4 Bakina ba zai faɗi ƙarya ba,Harshena kuma ba zai hurta maganganun yaudara ba.
5 Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
6 Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.
7 “Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.
8 Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?