5 Allah ya sawwaƙa in ce kun yi daidai,Har in mutu ba zan daina tsare mutuncina ba.
6 Ina riƙe da adalci kam, ba kuwa zan sake shi ba,Zuciyata ba ta zarge ko ɗaya daga cikin kwanakin raina ba.
7 “Bari maƙiyina ya zama kamar mugun mutum,Wanda ya tashi gāba da ni ya zama kamar marar adalci.
8 Wace sa zuciya take ga marar tsoron Allah?Sa'ad da Allah ya datse shi, ya ɗauke ransa?
9 Allah kuwa zai ji kukansa sa'ad da wahala ta same shi?
10 Ko Mai Iko Dukka zai zama abin farin ciki a gare shi?Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?
11 “Zan koya muku zancen ikon Allah,Abin da yake na wajen Mai Iko Dukka ba zan ɓoye ba.