1 “Hakika akwai ma'adinai na azurfa,Da wuraren da ake tace zinariya.
2 Mutane sukan haƙo baƙin ƙarfe daga ƙasa,Sukan narkar da tagulla daga dutse.
3 Mutane sukan kawar da duhu,Sukan kuma bincike zuzzurfar iyaka,Sukan haƙo duwatsun da suke cikin duhu, duhu baƙi ƙirin.
4 Sukan haƙa loto a fadama nesa da mutane,Sukan kafa abin lilo su yi ta lilo nesa da mutane.
5 “Daga cikin ƙasa ake samun abinci,Amma a ƙarƙashinta yakan zama kamar wuta.
6 Akwai duwatsu masu daraja cikin duwatsunta,Akwai zinariya a ƙurarta.