18 Kada ma a ko ambaci murjani,Da duwatsu masu walƙiya.Gama tamanin hikima ya fi na lu'ulu'ai mafiya daraja duka.
19 Ba za a daidaita tamaninta da na duwatsun tofaz na Habasha ba.Tamaninta ya fi na zinariya tsantsa.
20 “To, daga ina hikima ta fito?A wane wuri kuma haziƙanci yake?
21 Ba talikin da ya iya ganinta,Ko tsuntsun da yake tashi sama.
22 Halaka da Mutuwa sun ce,‘Da kunnuwanmu mun ji ƙishin-ƙishin a kanta.’
23 “Allah ne kaɗai ya san hanya zuwa gare ta,Ya san inda hikima take,
24 Saboda yana ganin duniya ɗungum,Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.