24 Saboda yana ganin duniya ɗungum,Yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sararin sama.
25 Sa'ad da Allah ya sa iska ta hura,Ya yi wa tekuna iyaka.
26 Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama,Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,
27 Shi ya san hikimar, shi ya sanar,Ya tabbatar da ita, ya bincike ta sarai.
28 “Allah ya ce wa mutane,‘Duba, tsoron Ubangiji shi ne hikima,Rabuwa da mugunta kuma, ita ce haziƙanci.’ ”