1 Ayuba ya ci gaba da magana.
2 Da ma ina cikin lokacin da ya wuce ne,Lokacin da Allah yake lura da ni,
3 Sa'ad da fitilarsa take haskaka mini,Ta wurin haskensa kuma nake tafiya da duhu,
4 Kwanakin da nake gaɓar raina,Lokacin da ni'imar Allah take kan gidana,
5 Sa'ad da Mai Iko Dukka yake tare da ni,'Ya'yana duka kuma suka kewaye ni,