13 Waɗanda suke bakin mutuwa sukan sa mini albarka,Na taimaki gwaurayen da mazansu suka mutu,Su raira waƙa don murna.
14 Adalci shi ne suturata,Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15 Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.
16 Ni mahaifi ne ga matalauta,Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.
17 Nakan karya muƙamuƙin marar adalci,In sa yă saki ganimar da yă kama.
18 “Da na zaci zan mutu cikin sutura,Kwanakina kuma su riɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,
19 Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa,Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana .