14 Adalci shi ne suturata,Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15 Ni ne idon makafi, guragu kuma, ni ne ƙafarsu.
16 Ni mahaifi ne ga matalauta,Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.
17 Nakan karya muƙamuƙin marar adalci,In sa yă saki ganimar da yă kama.
18 “Da na zaci zan mutu cikin sutura,Kwanakina kuma su riɓaɓɓanya, su yi yawa kamar yashi,
19 Saiwoyina a shimfiɗe suke cikin ruwa,Dukan dare raɓa na sauka a kan rassana .
20 Darajata garau take a gare ni,Bakana kullum sabo yake a hannuna.