1 Ayuba ya yi magana ya la'anci ranar da aka haife shi.
2 Ya ce,“Ya Ubangiji, ka la'anci ranan nan da aka haife ni.
3 Ka la'anci daren nan da aka yi cikina.
4 Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah.Kada a ƙara tunawa da wannan rana,Kada haske ya ƙara haskakata.
5 Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin.Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta.