15 Sun firgita ni,Sun kori darajata kamar da iska,Wadatata kuma ta shuɗe kamar girgije.
16 “Yanzu zuciyata ta narkeKwanakin wahala sun same ni.
17 Da dare ƙasusuwana karkaɗuwa suke,Azaba tana ta gaigayata ba hutawa.
18 An yi mini kamun kama-karya,An ci wuyan rigata.
19 Allah ya jefar da ni cikin laka,Na zama kamar ƙura ko toka,
20 “Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba,Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.
21 Ka zama mugu a gare ni,Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.