1 “Na yi alkawari da idanuna,Me zai sa in ƙyafaci budurwa?
2 Wane rabo zan samu daga wurin Allah a Sama?Wane gādo kuma zan samu daga wurin Mai Iko Dukka a can samaniya?
3 Yakan aika da masifa da lalacewaGa waɗanda suke aikata abin da ba daidai ba.
4 Allah ya san dukan abin da nake yi,Yana ƙididdige dukan takawata.