15 Ashe, shi wanda ya halicce ni a cikin mahaifa,Ba shi ne ya halicce su ba?Shi wanda ya siffata mu a cikin mahaifa?
16 “Ban taɓa ƙin taimakon matalauta ba,Ban kuma taɓa sa gwauruwar da mijinta ya mutu ta yi kuka ba,
17 Ko kuwa in bar marayu da yunwa sa'ad da nake cin abincina,
18 Tun suna yara nake goyonsu,Ina lura da su kamar 'ya'yan cikina.
19 “Amma idan na ga wani yana lalacewa saboda rashin sutura,Ko wani matalauci marar abin rufa,
20 Idan a zuciyarsa bai sa mini albarka ba,Ko bai ji ɗumi da ulun tumakina ba,
21 Ko na ɗaga hannuna don in cuci maraya,Don na ga ina da kafar kuɓuta,