24 “Idan na ce ga zinariya na dogara, ko zinariya tsantsa ita ce jigona,
25 Idan kuma saboda yawan dukiyata nake fariya,Ko saboda abin da na mallaka ne,
26 Idan ga hasken rana nake zuba ido,Ko ga hasken farin wata ne,
27 Zuciyata ta jarabtu ke nan a asirce,Ni da kaina ina sumbatar hannuna,
28 Wannan ma zai zama laifi ne wanda alƙalai za su hukunta,Gama na zama munafukin Allah Mai Iko Dukka ke nan.
29 “Idan na yi murna saboda wahala ta sami maƙiyana,Ko na yi fariya saboda mugun abu ya same shi,
30 Ban yi zunubi da bakina ba,Ban nemi ran wani ta wurin la'anta shi ba.