5 “Idan ina tafiya da rashin gaskiya,Ina hanzari don in aikata yaudara,
6 Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai,Zai kuwa san mutuncina.
7 Idan dai na kauce daga hanya,Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,
8 To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,Bari a tumɓuke amfanin gonata.
9 “Idan na yi sha'awar wata mace,Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10 To, bari matata ta yi wa wani abinci,Bari waɗansu su kwana da ita.
11 Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,Wanda alƙalai ne za su hukunta.