6 Bari Allah ya auna ni da ma'aunin da yake daidai,Zai kuwa san mutuncina.
7 Idan dai na kauce daga hanya,Ko kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna,Idan akwai ko ɗan sofane a hannuna,
8 To, bari in shuka, wani ya ci amfanin,Bari a tumɓuke amfanin gonata.
9 “Idan na yi sha'awar wata mace,Har na je na laɓe a ƙofar maƙwabcina,
10 To, bari matata ta yi wa wani abinci,Bari waɗansu su kwana da ita.
11 Gama wannan mugun laifi ne ƙwarai,Wanda alƙalai ne za su hukunta.
12 Za ta zama wuta mai ci har ta hallaka,Za ta cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.