8 Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum,Yakan ba mutane basira.
9 Ba tsofaffi ne masu wayo ba,Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai yake gane abin da yake daidai ba.
10 Don haka na ce ku kasa kunne gare ni,Bari in faɗa muku nawa ra'ayi.
11 “Ga shi, na dakata na ji maganarku,Na kasa kunne ga maganarku ta hikima,Tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.
12 Na kasa kunne gare ku sosai,Amma ko ɗaya ba wanda ya kā da Ayuba.Ba kuma wanda ya ba shi amsar tambayarsa.
13 Ku lura kada ku ce kuna da hikima,Allah ne kaɗai yake da iko ya kā da shi, ba mutum ba.
14 Ba da ni Ayuba yake magana ba,Saboda haka ba zan amsa masa da irin amsarku ba.