1 “Amma yanzu, kai Ayuba, ka yarda ka ji maganata,Ka kasa kunne ga dukan abin da zan faɗa.
2 Ga shi, na buɗe baki in yi magana.
3 Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce,Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
4 Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5 “Ka amsa mini, in ka iya,Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6 Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.