2 Ga shi, na buɗe baki in yi magana.
3 Maganar da zan hurta ainihin gaskiyar da take a zuciyata ce,Abin da zan faɗa kuma dahir ne.
4 Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5 “Ka amsa mini, in ka iya,Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6 Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.
7 Don haka kada ka razana saboda ni,Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
8 “Hakika na ji maganar da ka yi,Na kuwa ji amon maganganunka,