30 Don ya komo da ran mutum daga kabari,Domin a haskaka shi da hasken rai.
31 “Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne,Ga abin da nake faɗa,Ka yi shiru, zan yi magana.
32 Amma idan kana da ta cewa, to, amsa,Yi magana, gama ina so in kuɓutar da kai.
33 In kuwa ba haka ba, sai ka yi shiru,Ka kasa kunne gare ni,Zan kuwa koya maka hikima.”