4 Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
5 “Ka amsa mini, in ka iya,Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
6 Duba, ni da kai ɗaya muke a wajen Allah,Dukanmu biyu kuma daga yumɓu aka siffata mu.
7 Don haka kada ka razana saboda ni,Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
8 “Hakika na ji maganar da ka yi,Na kuwa ji amon maganganunka,
9 Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi,Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.
10 Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,