1 Elihu ya ci gaba.
2 “Ku mutane masu hikima, ku ji maganata,Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
3 Kunne yake rarrabewa da magana,Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.
4 Bari mu zaɓi abin da yake daidai,Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.
5 Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne,Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
6 Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci,Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.’