23 Ba ajiyayyen lokacin da ya ajiye wa kowane mutumDa zai je shari'a a gaban Allah.
24 Yakan ragargaza ƙarfafa ba tare da wani bincike ba,Ya sa waɗansu a madadinsu.
25 Saboda sanin ayyukansu,Yakan kaɓantar da su da dare ya ragargaza su,
26 Yakan buge su a gaban mutane saboda muguntarsu,
27 Don sun daina binsa, ba su kula da ko ɗayaDaga cikin umarnansa ba.
28 Suka sa matalauta su yi kuka ga Allah,Ya kuwa ji kukan waɗanda ake tsananta wa.
29 Idan Allah zai yi shiru, da wa zai sa wa wani laifi?Idan ya ɓoye fuskarsa, wa zai iya ganinsa,Ko aka yi wa al'umma ko ga mutum?