6 Duk da rashin laifina an ɗauke ni a maƙaryaci,Raunina ba ya warkuwa ko da yake ba ni da laifin kome.’
7 “Wane irin mutum ne kai, Ayuba,Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,
8 Wanda yake cuɗanya da ƙungiyar masu aikata laifi,Kana yawo tare da mugaye?
9 Gama ka ce, ‘Bai amfana wa mutum kome baYa yi murna da Allah.’
10 “Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai,Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne,A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,
11 Gama bisa ga aikin mutum yake sāka masa,Yana sa aniyarsa ta bi shi.
12 Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba,Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.