1 Elihu kuwa ya yi magana.
2 “Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce,Ba ka yi laifi a gaban Allah ba,
3 Ka kuwa ce, ‘Wace riba na ci?Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?’
4 Zan ba ka amsa, kai da abokanka.
5 Ka duba sama,Ka dubi gizagizai waɗanda suke can sama da kai.