6 Idan ka yi zunubi, da me ka cuci Allah?Idan ka aikata laifofi da yawa, wace cuta ka yi masa?
7 Idan kai adali ne da me ka ƙara masa,Ko kuwa me ya samu daga gare ka?
8 Muguntarka ta shafi mutum ne kamarka,Haka kuma adalcinka ya shafi ɗan adam ne kawai.
9 “Saboda yawan zalunci, jama'a sukan yi kuka,Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi.
10 Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba,Wanda yakan sa a raira waƙa da dare,
11 Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya,Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima.
12 Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba,Saboda suna da girmankan mugaye.