1 Elihu ya ci gaba da magana.
2 “Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka,Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah.
3 Zan tattaro ilimina daga nesa,In bayyana adalcin Mahaliccina.
4 Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba,Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai.
5 “Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa,Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira.
6 Ba ya rayar da masu laifi,Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu.
7 Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya,Yakan kafa su har abada tare da sarakuna,A gadon sarauta, ya ɗaukaka su.