19 Kukanka ya iya raba ka da wahala,Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi?
20 Kada ka ƙosa dare ya yi,Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse,Kowa ya kama gabansa.
21 Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta,Gama saboda haka kake shan wannan tsanani,Don a tsare ka daga aikata mugunta.
22 “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa,Wa ya iya koyarwa kamarsa?
23 Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi,Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure?
24 “Ka tuna ka girmama aikinsa,Wanda mutane suke yabo.
25 Dukan mutane sun ga ayyukansa,Sun hango shi daga nesa.