23 Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi,Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure?
24 “Ka tuna ka girmama aikinsa,Wanda mutane suke yabo.
25 Dukan mutane sun ga ayyukansa,Sun hango shi daga nesa.
26 Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne,Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba,Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27 “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi,Ya maishe shi ruwan sama,
28 Wanda yakan kwararo daga sama,Ya zubo wa ɗan adam a yalwace.
29 Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,Da tsawar da ake yi a cikinsu?