29 Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama,Da tsawar da ake yi a cikinsu?
30 Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi,Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu.Zurfin teku yana nan da duhunsa.
31 Gama ta haka yakan shara'anta mutane,Yakan ba da abinci a yalwace.
32 Ya cika hannunsa da walƙiya,Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.
33 Tsawarta tana nuna kasancewar Allah,Ko shanu sun san da zuwan hadiri.”